Home Addini A Jigawa an bada hutun sabuwar shekarar Musulunci

A Jigawa an bada hutun sabuwar shekarar Musulunci

143
0

Gwamnatin jihar Jigawa ta bi sahun maƙwabciyarta jihar kano wajen bayyana Alhamis 1 ga watan Muharram 1442 bayan Hijira a matsayin ranar hutu a faɗin jihar domin taya al’ummar musulmi murna zagayowar shekarar musulunci.

Gwamna Badaru Muhammad Abubakar na jihar, ya taya iahirin al’ummar musulmin jihar murnar shiga sabuwar shekarar, ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su yi koyi da koyarwar addinin musulunci.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan jihar da su yi amfani da wannan rana ta hutu domin gudanar da addu’o’i domin samun zaman lafiya da ma ɗorewar arziƙi a faɗin jihar dama ƙasa baki ɗaya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply