Home Labarai A karo na biyu, majalisar wakilai ta buƙaci hafsoshin tsaro su yi...

A karo na biyu, majalisar wakilai ta buƙaci hafsoshin tsaro su yi murabus

121
0

‘Yan majalisar wakilai ta tarayya sun nuna bacin ran su kan ci gaba da hare-haren Boko Haram da ake samu a Nijeriya, inda suka ce dole ne hafsoshin tsaron kasar su yi murabus.
Wannan dai shi ne karo na biyu da ‘yan majalisar suka kada kuri’ar debe kauna da hafsoshin tsaron.
Kiran da ‘yan majalisar suka yi a zaman ta na jiya Talata, ya biyo bayan kudirin da Yusuf Buba daga Adamawa ya gabatar kan harin garin Garkida da ke karamar hukumar Gumbi na jihar.
Buba ya ce a halin yanzu hafsoshin tsaron ba su da wata sabuwar basirar yadda za a magance ayyukan na Boko Haram.
Da yake bada tashi gudunmuwa, Ahmed Jaha daga jihar Borno ya ce idan har aka kasa magance matsalar ‘yan ta’adda a kasar zai yi murabus daga kujerar sa.
Shima Karu Simon Elisha daga Gombe, cewa ya yi Nijeriya na bukatar dubaru na yaki da ta’addanci wanda hafsoshin tsaron suka kasa samarwa.
Da ake aiwatar da kudirin, majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta fara daukar ‘yan Nijeriya aikin soji don yaki da matsalar.
Majalisar ta kuma umarci hukumar bada agaji ta kasar NEMA da hukumar ci gaban yankin Arewa maso gabas da su kai kayan tallafi ga wadanda harin Garkida da na Auno a jihar Bornon.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply