Yanzu haka mataimakin shugaban majalisar Dattawa Ovie Omo-Agege na shugabantar zaman majalisar dattawan Nijeriya.
Wannan dais hi ne karon farko da Omo-Agege ke jan ragamar majalisar a cikin watanni 7 da rantsar da shi a matsayin mataimakin shugaban majalisar.
Ya zauna kan kujerar shugabancin majalisar na yau ne da misalin karfe 11:30am na safiyar yau, bayan da shugaban majalisar Ahmad Lawan ya fita don halartar wasu harkokin a wajen majalisar.
Har yanzu dai zaman majalisar na ci gaba da gudana.
