Home Sabon Labari Jonathan ya rinka sauraran masu fada masa karya- Reuben Abati

Jonathan ya rinka sauraran masu fada masa karya- Reuben Abati

157
0

Reuben Abati tsohon mai magana da yawun Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya ce abu guda da zai iya cewa Goodluck Jonathan ya yi da bai amince da shi ba shi ne yadda Jonathan ke sauraran mutane su fada masa kary karara.

Reuben Abati a cikin wata tattaunawa ta Instagram Live da wata ‘yar jarida Josey Mahachie da ke zaune a Jamus a ranar Lahadi, ya ce tawalu’un Goodluck Jonathan ya sa koda an fada masa karya ba ya damuwa.

Reuben Abati

Abati ya ce wannan dabi’a ta Jonathan ta rinka daure masa kai domin akwai lokacin da idan masu fada masa karya sun wuce ya kan ce masa Shugaban Kasa karya aka fada maka amma cikin tawalu’u sai Goodluck ya ce shi ba dan siyasa bane, a siyasa sai ka saurari mutum ko wace irin dabi’a ya zo maka da ita.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply