Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta sassauta dokar hana fita da ta sanya wa jihar na tsawon kwanaki 14.
A ranar Litinin ne dai Shugaba Buhari ya sanar da kulle jihar, a wani mataki na daƙile yaɗuwar cutar coronavirus a jihar.
Sai dai da yake magana a gidan gwamnatin jihar lokacin ƙaddamar da wani ƙaramin kwamiti da zai taimaka wa kwamitin yaƙi da cutar a jihar, Ganduje ya ce yana da muhimmanci a sassauta dokar a daidai wannan lokaci duba da mawuyacin halin da jama’a ke ciki.
