Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Abia Chief Johnson Onouigbo, ya mutu.
Mr Onuigbo da aka fi sani da “Akinbod” ya mutu ne a yammacin Litinin a birnin Umuahia bayan gajeruwar rashin lafiya.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa ba a bayyana musabbabin mutuwarsa ba, amma dai an ajiye gawarsa a wani wurin da ba kowa ya sani ba a cikin asibitin Umuahia.
