Home Sabon Labari ABIN TAKAICI: an sace matar babban jami’in gwamnan Ondo

ABIN TAKAICI: an sace matar babban jami’in gwamnan Ondo

152
0

Rahotanni daga jihar Ondo sun tabbatar da cewa an sace matar Olugbenga Ale, shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Ondo.

An sace Mrs Ale tare da direbanta da kuma wani mutum daya dan rakiyarsu, a kan babban titin Ondo-Akure a yankin Owen da ke karamar hukumar Idanre ta jihar a daren Alhamis din makon nan.

Hakan ya faru ne kasa da sa’o’i 24 da kisan Oba Adegoke Adeusi, basaraken gargajiyar Ifon ta karamar hukumar Ose a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply