Home Coronavirus Abu ɗaya zai hana mu sake kulle Nijeriya – PTF

Abu ɗaya zai hana mu sake kulle Nijeriya – PTF

121
0

Kwamitin shugaban kasa kan cutar COVID-19 PTF, ya ce yanayin yadda ‘yan Nijeriya ke tsare ka’idojin hana yaduwar cutar ne kadai zai iya tantance ko za a sake kafa dokar kulle ko a’a.

Jami’in tsare-tsaren kwamitin DR. Sani Aliyu ne ya sanar da hakan a ranar Talata, yana mai cewa babu wani mataki da aka cimmawa kan dokar kullen har yanzu.

Idan za a iya tunawa a watan Maris na shekarar da ta gabata gwamnatin tarayya ta saka dokar kulle a babban Birnin tarayya Abuja da jihohin Lagos da Ogun, na tsawon sama da mako biyar sakamakon barkewar annobar COVID-19 a karon farko.

A makon jiya, gwamnatin tarayya ta ce ba ta da wani zabi da ya wuce sake kafa dokar, idan adadin masu kamuwa da cutar ya ci gaba da karuwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply