Home Labarai Abu ne mawuyaci a iya tantance yawan jama’ar Nijeriya – NPC

Abu ne mawuyaci a iya tantance yawan jama’ar Nijeriya – NPC

133
0

Hukumar ƙidaya ta Nijeriya NPC ta ce abu ne mawuyaci a iya tantance haƙiƙanin yawan jama’ar ƙasar sakamakon rashin gudanar da aikin ƙidayar jama’a da ba a yi ba cikin shekaru 14 da suka wuce.

Shugaban hukumar ta NPC Nasir Kwarara wanda ya bayyana haka ranar Talata a Abuja, ya ce yanzu haka hasashen yawan jama’ar ƙasar ya kai miliyan 206.

Wannan dai na zuwa ne shekaru biyu daidai, bayan da hukumar ƙidayar ta ƙiyasta yawan mutanen Nijeriya a miliyan 198.

Kwarra ya ce shugaba Buhari shi kaɗai ke da hakƙin bayyana ranar da za a sake gudanar da ƙidayar jama’a, a ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply