Home Labarai Jami’ar ABU Zaria za ta bude karatu a ranar 25.01.2021

Jami’ar ABU Zaria za ta bude karatu a ranar 25.01.2021

72
0

Hukumar gudanarwar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a taronta karo na 501 ta saka ranar 25 ga watan Janairu, 2021 a matsayin ranar sake bude jami’ar don cigaba da karatu.

A cikin wata sanarwa daga daraktan watsa labaran jami’ar Malam Auwalu Umar, tace wannan matakin zai yi aiki ne da umurnin da gwamnatin tarayya da ta Kaduna za su bayar nan gaba game da sake bude jami’o’in.

Sanarwar ta ce an yanke shawarar sake bude jami’ar ne bayan janye yajin aiki da ASUU ta yi da kuma umurnin da hukumar NUC ta bayar na a sake bude jami’o’i. Ta kuma ce za a kammala zangon karatu na 2019/2020 dai-dai da yadda tsarin karatun zai cigaba.

Sanarwar tace daliban shekarar karshe ne za su fara komawa da ‘yan aji daya da biyu da daliban sashen kiwon lafiya da sauransu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply