Home Sabon Labari Abun da ya sa Diego Costa ya bar Atletico Madrid

Abun da ya sa Diego Costa ya bar Atletico Madrid

100
0

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta sanar da warware yarjejeniya tsakaninta da dan wasanta, Diego Costa a ranar Lahadi.

Costa ne ya aike wa kungiyar bukatar hakan, ita kuma kungiyar ta amince bayan duba bukatar tasa.

Shekara ta 2020 dai ta kawo wa Costa tsaiko da koma baya, inda ya sha fama da jinyar raunuka da ya samu, daga baya-bayan nan kuma ya harbu da cutar COVID-19.

Sanarwar ta kawo karshen zamansa a kungiyar a karo na biyu.

Costa ya bar kungiyar zuwa Chelsea a 2014, inda ya zura kwallaye 64 a wasanni 134 da ya buga mata.

Sai dai bayan dawowarsa Madrid a karo na biyu, Costa ya zura kwallaye 19 a cikin wasanni 81 da ya buga.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply