Home Labarai Adamawa: ‘Yan mata Na Bukatar A Yi Dokar Hana Auren Wuri

Adamawa: ‘Yan mata Na Bukatar A Yi Dokar Hana Auren Wuri

93
0

Abdullahi Garba Jani

‘Yan mata a jihar Adamawa sun yi kira ga uwargidan gwamnan jihar Hajiya Lami Fintiri da ta yi kokarin Samar da hanyar da za a yi dokar hana auren wuri ga yara mata kanana

‘Yan matan sun yi wannan koken ne a cikin wata takardar da suka mika ma ta bayan rangadin bikin ranar ‘ya’ya mata ta duniya da aka yi a Yola.

Da ta ke karanta takardar a madadin sauran yaran, Fatima Isma’ila ta ce samar da dokar ya zama wajibi don ba ‘ya’ya mata damar samun sukunin neman ilmi.

Yaran sun kuma yi kira da a kara daukar malaman makaranta mata kuma a ware tsakanin makewayin mata da na maza a makarantu.

Kazalika, sun kuma roki da a ba su kariya daga musgunawa, fyade da sauran hanyoyin cin zarafinsu a jihar.

Da ta ke mai da jawabi, uwargidan gwamnan jihar Hajiya Lami Fintiri ta ba su tabbacin cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen ci gaban ilmi musamman na ‘ya’ya mata a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply