DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 10, 2026
HomeSiyasaADC ta yi alkawarin za ta kawo karshen almubazzaranci a gwamnati idan...

ADC ta yi alkawarin za ta kawo karshen almubazzaranci a gwamnati idan ta ci zaɓen 2027

Jam’iyyar ADC ta yi alkawarin soke tsarin ɓatar da kuɗaɗen “security vote” da ba ya samun cikakken sa ido daga majalisa, idan ta samu damar kafa gwamnati bayan zaɓen 2027.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin kundinta mai shafuka 25 mai suna The Orange Book, wanda sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya gabatar a Abuja ranar Talata.

ADC ta ce duk wani kuɗin da za a ware domin tsaro zai kasance ƙarƙashin cikakken tsarin, amincewa da binciken majalisa, domin rage yiwuwar karkatar da kuɗaɗen gwamnati.

Jam’iyyar ta kuma yi alkawarin rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen tafiye-tafiyen jami’an gwamnati, inda ta ce za a takaita tafiye-tafiye zuwa waɗanda suke da muhimmanci kuma suke da alaƙa kai tsaye da ayyukan gwamnati.

A cewar jam’iyyar, ba za a yarda jami’ai su riƙa tafiye-tafiye da iyalansu ko abokan siyasa a matsayin tawaga ta gwamnati ba, sannan za a takaita alawus-alawus da kuɗin tafiye-tafiye zuwa matakan da hukumomin da abin ya shafa suka amince da su.

ADC ta kuma ce motocin gwamnati, gidaje, jiragen sama, ofisoshi da sauran kadarorin gwamnati da aka bai wa jami’an siyasa za a yi amfani da su ne kawai wajen ayyukan hukuma.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa za ta ɗauki duk wani nau’in wawure wa ko karkatar da dukiyar gwamnati a matsayin babban laifi, inda ta bayyana cewa “duk wani nau’in wawure dukiyar jama’a za a ɗauke shi a matsayin wani nau’in fashi da tsinin biro.”

Baya ga batun kashe kuɗaɗen gwamnati, ADC ta yi alkawarin ƙarfafa hukumomin gwamnati, ciki har da ƙara ‘yancin kai ga bangaren shari’a, majalisa da hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), tare da ƙara kariya ga masu tona asirin almundahana.

Jam’iyyar ta kuma ce za ta mayar da hankali wajen samar da tattalin arzikin da ke haifar da ayyukan yi da damar samun arziki, tare da ƙarfafa kamfanoni masu zaman kansu da kuma hana tsarin son kai, monopolies da cronyism.

A bangaren ilimi kuwa, ADC ta ce za ta daidaita tsarin ilimi da buƙatun tattalin arziki da fasaha domin samar da ƙwarewar da za ta taimaka wajen bunƙasa ƙasar.

A yayin gabatar da kundin, Abdullahi ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da gazawa wajen samar da kyakkyawan shugabanci, inda ya yi wasu kalamai masu zafi kan yadda yake ganin gwamnatin ta na tafiyar da ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata