Home Labarai AfDB Zai samar da tallafi ga matan Afirika

AfDB Zai samar da tallafi ga matan Afirika

73
0

Bankin ci gaban Afirika AfDB, ya amince da kafa wata gidauniya da za ta tallafawa mata da samar da daidaito a ƙasashen Afirika.

Gidauniyar za ta taimaka musamman wajen tabbatar da mata na samun tallafin da Bankin ke badawa a ƙarƙashin shirin sa na tallafin kuɗi ga mata watau AFAWA da kuma samar da daidaito wajen bada rance.

Wannan dai shi ne karon farko da Bankin ya samar da wasu kuɗi kan jinsi.

Wata sanarwa da Bankin ya fitar ya ce za a samar da kashin farko na kuɗin ne nan da shekara 10.

Daga cikin waɗanda za su tallafawa shirin akwai ƙasashen Netherlands, Faransa da Birtaniya.

Bankin AfDB dai, ya ɓullo da shirin AFAWA ne, don cike giɓin ratar da aka ba matan Afirika a ɓangaren kuɗi da ta kai Dala Biliyan $42.

Ta hanyar wannan tallafi dai, matan Afirika za su samu babbar damar shiga kasuwanci da shiga a dama da su a harkokin ci gaban tattalin arziƙi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply