Home Kasashen Ketare Afghanistan: ‘Yan Taliban sun sace ‘yan jarida 6

Afghanistan: ‘Yan Taliban sun sace ‘yan jarida 6

83
0

Abdullahi Garba Jani/dkura

 

‘Yan kungiyar Taliban sun sace ‘yan jarida 6 da ke aiki a kafafen watsa labarai na gwamnati da masu zaman kansu a Arewacin lardin Paktia na kasar Afghanistan, kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

 

An sace ‘yanjaridar da ke aiki da gidajen rediyo da talabijin daban-daban a lokacin da suke kan hanyarsu daga lardin Paktia zuwa wani makwabcin lardin don halartar taron bita a ranar Juma’a.

 

Mai magana da yawun gwamnan lardin Paktia Abdullahi Hasrat ya ce ana nan ana tattaunawa da wadanda suka sace su don samu a kubutar da su.

Hotan wani shugaban kungiyar Taliban

A wani labarin ma, mai magana da yawun kungiyar Taliban ya tabbatar da cewa mayakan sun kama ‘yanjaridar amma dai za a sako su nan ba da jimawa ba.

 

Ya ce ya zuwa yanzu layin waya ba ya tafiya, amma da zarar sun samu layi, za su gana da masu ruwa da tsaki don ganin an sako su.

 

Kasar Afghanistan ce dai kasa mafi hatsari a duniya ga ‘yanjarida a shekarar 2018 inda’yanjarida 13 suka mutu.

 

Cibiyar ‘yanjarida ta duniya ta ce an kashe ‘yanjarida 16 a shekarar bara. Ko a watan Yuli, kungiyar Taliban ta yi barazana ga kasar kafafen watsa labaran kasar  Afghanistan cewa za ta fara kai hari ga ‘yanjarida madamar ba su dai na yada abin da suka kira farfagandar gwamnati ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply