Bankin duniya ya yi hasashen cewa ƙasashen Afirika za su fuskanci mummunan koma bayan tattalin arziƙi a shekarar 2020 sakamakon ɓarkewar cutar coronavirus.
Wani rahoto da bankin ya fitar jiya Alhamis ya ce ƙasashen na yankin Sahara za su samu faɗuwar tattalin arziƙi da ba a taɓa samun irin ta ba tun bayan rikicin tattalin arziƙi na farko da Nahiyar ta shiga shekaru 25 da suka wuce.
A cewar rahoton tattalin arziƙi na bankin duniyar, ƙasashen Afirika za su yi asara daga Dala Biliyan 37 zuwa Dala Biliyan 79 a bana.
Rahoton ya ce ɓarkewar cutar zai mayar da hannun agogo baya ga ci gaban da tattalin arziƙin Nahiyar fiye da ninkin ci gaban da aka samu a shekarar 2019.
Da yake sharhi kan rahoton mataimakin shugaban bankin duniya a Nahiyar Afirika Hafez Ghadem ya ce ƙasashen Afirika su ne za su fi ji a jikin su sakamakon ɓarkewar cutar da take ci gaba da mamaye duniya.
Marubuta rahoton sun ce duk da cewa halin da ake ciki yanzu ya janyo koma baya a dukkan ɓangarori, amma lamarin zai fi yin illa ne a manyan ƙasashen da suka fi ci gaban tattalin arziƙi a Nahiyar watau Nijeriya, Angola da Afirika ta Kudu saboda koma bayan da suke fuskanta na tattalin arziƙi da zuba jari.
