Home Labarai Afuwa: Masu sukar Gwamna Matawalle ba su da adalci – Lai

Afuwa: Masu sukar Gwamna Matawalle ba su da adalci – Lai

24
0

Ministan yada labarai da al’adu na Nijeriya Lai Mohammed, ya ce ba adalci ba ne a rika sukar matakin Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, na yin afuwa ga ‘yanbindigar da suka addabi yankin Arewa maso Yammacin kasar.

Ministan wanda ya yake magana a wani shirin talabijin, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta dakatar da gwamnonin ba, daga kokarin da suke na magance matsalar tsaro a jihohinsu daidai yadda suke ganin ya dace da jihohin.

A cewarsa, yanayin matsalar tsaron ta sha banban a jihohin, kuma gwamnoni su ne shugabannin tsaron jihohinsu, don haka su suka fi dacewa su samar da tsarin da za samu mafita ga matsalolin.

A cikin makon nan ne dai Gwamnan na Zamfara ya yi afuwa ga shahararren dan ta’addan nan, Auwalun Daudawa, wanda ya jagorancin sace sama da dalibai 300 a Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Kankara a karshen shekarar bara.

Gwamnatin tarayya da wasu gwamnatocin jihohi dai na amfani da shirin afuwar, wanda ya kunshi gyaran hali ga masu aikata laifi tare da maida su yin rayuwa cikin al’umma kamar kowa.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply