Home Labarai A’isha Buhari ta ba da tallafin cocila ga ‘yan gudun hijrar Katsina

A’isha Buhari ta ba da tallafin cocila ga ‘yan gudun hijrar Katsina

315
0

Uwargidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta ba da gudunmuwar fitilar tocila ga ‘yan gudun hijrar da ke karamar hukumar Batsari jihar Katsina.

Uwargidan shugaban kasar, ta hannun kwamishinar harkokin mata ta jihar Katsina ta ce an ba da gudunmuwar fitilar ne domin ‘yan gudun hijrar su samu damar haska inda suke zaune kasantuwar suna bakon wuri.

Kwamishinar ta ce uwargidan shugaban kasar ta kuma ba da gudunmuwar takalman silifas sabo da shiga bandaki.

Bugu da kari, akwai gudunmuwar shinkafa, man girki, taliyar indomie, da sabulun wanka duk ga ‘yan gudun hijrar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply