Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya Aisha Buhari ta tafi Hadaddiyar Daular Larabawa (Dubai) domin duba lafiyarta.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a lokacin hutun sallah babba uwargidan shugaban kasar ta bar Nijeriya.
Rahotanni sun ce Aisha Buhari na fama da ciwon wuya, bayan da ta koma Abuja daga Lagos.
