Home Kasashen Ketare Akwai Alamun Shigo-Shigo Ba Zurfi A Tafiyar ‘Yan wasana-inji Solskjaer

Akwai Alamun Shigo-Shigo Ba Zurfi A Tafiyar ‘Yan wasana-inji Solskjaer

78
0

Ahmadu Rabe/Jani

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solkjaer ya yi Allah wadai da rashin kwazon ‘yan wasansa, ya kuma zarge su da kokarin haddasa fitinar yadda kungiyar za ta sallame shi daga bakin aiki.

Tuni dai dangantaka ta yi tsami tsakanin Solkjear da ‘yan wasan nasa tun, bayan kashin da kungiyar ta sha a hannun kungiyar Newcastle a gasar Premier a karshen mako nan.

A halin yanzu solkjear na fuskantar matsin lamba a kungiyar tasa, an kuma umarce shi da ya gaggauta gyara matsalolin da suke fuskanta, duk da cewar a watan jiya, mataimakin shugaban kungiyar Ed Woodward ya ce zai ci gaba da mara mi shi baya.

Ko a cikin satin nan an yi ta rade-radin United din zata sallami Solkjaer cikin wannan wata, muddin kungiyar ta sha kaye a wasan da za ta fafata da Norwich City a ranar 20 ga Oktoba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply