Gwamnatin Nijeriya ta ce akwai yiwuwar tattalin arzikin kasar ya kara shiga garari nan da shekaru 4 masu zuwa muddin babu wasu kwararan matakan da aka dauka na kare afkuwar hakan.
Karamin ministan kasafin kudi da tsare-tsare Clem Agba ne ya yi wannan furucin a lokacin taron hadin guiwa na kwamitin kudi da tsarin tattalin arziki.
Ya ce ma’aunin tattalin arzikin Nijeriya na GDP ba ya da wani katabus a halin yanzu, don haka ne muddin aka yi sake, to kuwa nan da shekaru 4 masu zuwa za a samu damuwa.
