Home Addini Akwai bukatar ci gaba da adu’o’in dorewar zaman lafiya a Nijeriya-Gwamna Sule

Akwai bukatar ci gaba da adu’o’in dorewar zaman lafiya a Nijeriya-Gwamna Sule

72
0

Abdullahi Garba Jani

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya yi kira ga musulman Nijeriya da su ci gaba da adu’o’in dorewar zaman lafiya da hadin kai a kasar.

Gwamnan Abdullahi Sule ya yi wannan kiran ne a lokacin bikin bude masabakar karatun Alqur’ani mai tsarki karo na 23 da kungiyar Izala ta shirya a birnin Lafiya.

Ya ce babu abin da kasar nan ke bukata da ya wuce adu’a don ta samu zaman lafiya, ya kuma yi kira ga al’umma musulmi da su hada kansu su yi adu’a ga kasar.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar Izala Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ana shirya masabakar karatun Alqur’anin ne a duk shekara don hada kan musulmai kuma su ji su karanta kalmomin Allah Madaukakin Sarki.

Sheikh Jingir ya ce kwananki 6 da za a kwashe ana masabakar, za su ba misulmi damar su sanin alfanun hadin kai da zaman lafiya..

Ya tabbatar da cewa musulmai a wurin za a su yi amfani da zaman da za su yi don yi wa Nijeriya adu’ar hadin kai da dorewar zaman lafiya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply