Home Labarai Akwai masu cutar HIV sama da 20,827 a Ogun – Kwamishina

Akwai masu cutar HIV sama da 20,827 a Ogun – Kwamishina

73
0

Kwamishinan lafiya na jihar Ogun Dr Tomi Coker yace har yanzu jihar ce kan gaba wajen masu dauke da cutar HIV a jihohin kudu maso yamma da yawan mutane sama da 20,827.

Dr Coker na magana ne a garin Abeokuta, a wajen taron manema labarai don bikin ranar cutar HIV ta duniya ta 2020.

Yace a jimilce, an samu karin masu dauke da cutar 105 a lokacin dokar zaman gida ta “lockdown”.

Kwamishinan lafiyar yace jihar nada kaso 1.6% sai jihohin Lagos mai kaso 1.4%, Ondo-1.1%, Oyo-0.9% da Osun-0.9%.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply