Home Labarai Akwai masu tabin hankali kusan milyan 50 a Nijeriya-Likita

Akwai masu tabin hankali kusan milyan 50 a Nijeriya-Likita

70
0

 

Abdullahi Garba Jani/Dutsenkura

Babban likitan asibitin masu tabin hankali na birnin Maiduguri Dr Ibrahim Wakawa, ya ce ‘yan Nijeriya kusan milyan 50 na fama da matsalar tabin hankali.

Dr Ibrahim Wakawa, ya yi wannan furucin ne a taron kokarin ganin an aiwatar da tsarin kiwon lafiya na gwamnatin jihar Borno a birnin Maiduguri.

Babban likitan ya alakanta yawan samun matsalar tabin hankalin da rikice-rikice, karancin fadakarwa da wayar da kai da kayan aikin da za a rika tunkarar wadannan matsalolin.

Dr Wakawa ya ce bincike ya nuna cewa mutum daya daga cikin mutane 4 na fama da matsalar kwakwalwa.

Ya ce asibitinsu na Maiduguri na kula da lafiyar mutane kusan milyan 30 daga shiyyar arewa maso gabashin Nijeriya kawai.

Ya ci gaba yana cewa kusan kuma kaso 60% na mutanen da ke zuwa kananan asibitoci na fuskantar matsalar tabin hankali.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply