Home Labarai Akwai sauran gwamnonin PDP da za su dawo APC – Gwamnan Kogi

Akwai sauran gwamnonin PDP da za su dawo APC – Gwamnan Kogi

81
0

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ce akwai sauran gwamnonin jam’iyyar PDP da ke kan hanyar komawa jam’iyyar APC.

Bello ya faɗi haka ne lokacin da yake magana kan komawar gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi jam’iyyar APC, lokacin da ake fira da shi a wani shirin siyasa na Channels TV a ranar Alhamis.

Bello ya ce APC na ƙoƙarin samar da ɗan takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023 wanda zai haɗa kan Nijeriya kuma kowa zai yarda da shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply