Home Labarai Akwai tabin hankali tattare da masu shan sigari – Bincike

Akwai tabin hankali tattare da masu shan sigari – Bincike

130
0

Wasu likitoci da ke jami’ar ‘St. Louis’ sun bayyana cewa masu fama da tabuwar hankali sun fi masu cikakken hankali yawan shan taba sigari.

A rahoton da jaridar “Leadership Ayau” ta wallafa ta ce likitocin sun gano haka ne a bincike da suka yi kan wasu da ke fama da tabuwar hankali da ake kula da su. A nan ne suka ga cewa lallai masu dan matsala a kwakwalwar su, sun fi shan taba fiye da wadanda ba haka ba.

Jagoran binciken Li-Shiun Chen ya ce mafi yawan masu shan taba suna son su bari amma hakan ya gagara. Sannan kuma idan har ma sun warke daga cutar ma rabuwa da tabar ya kan gagara.

Li-Shiun Chen ya yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya na asibitocin masu tabin hankali da su taimaka musu wajen ganin sun kubuta daga wannan dabi’a wato shan taba sigari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply