Home Addini Akwai yiwuwar a halasta luwadi a Gabon

Akwai yiwuwar a halasta luwadi a Gabon

174
0

Majalisar dattawan kasar Gabon ta kada kuri’ar amincewa da yi wa dokar haramta luwadi kwaskwarima mako guda bayan majalisar wakilan kasar ta amince da yin gyaran da zai ba da damar halasta luwadin.

Idan har kudirin ya samu sahalewar majalissun biyu kasar Gabon din za ta zama kasa ta farko a Afirka da ta halasta yin luwadi.

Tun a shekarar bara ne dai kasar ta amince da dokar daurin watanni 6 ga duk dan kasar da aka samu da aikata luwadi kafin yanzu da kasar ke shirin sauya wannan doka idan har ‘yan majalissun suka amince mata.

Tuni dai malaman addinin kasar suka fara yin tir da wannan matsaya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply