Home Kasashen Ketare Akwai Yiwuwar Bullar Cutar Ebola A Kasar Tanzania- WHO

Akwai Yiwuwar Bullar Cutar Ebola A Kasar Tanzania- WHO

77
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”bf836dlbu” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”avfjhfh2kg” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”ltt7kg6q8″ animation_delay=”0″]

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce kasar Tanzania na kin ba da cikakken bayani game da bullar cutar Ebola. A cikin wata takarda daga hukumar kula da lafiya ta fitar ta ce duk da roko da sauran mika bukatun da ta yi ga kasar, amma abin ya ci tura. Takardar ta ce duk wani abu da ake bukata dangane da cutar Ebola a kasar Tanzania ba ya samuwa.

 

Tuni dai ana ci gaba da alamtar da hukumomin da ke gabashi da tsakiyar nahiyar Afirka na barazanar bullar cutar ta Ebola daga kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo a inda ta kashe mutane sama da dubu biyu 2,000 a shekara guda.

 

Razani ya fara a kasar Tanzania na yiwuwar bullar cutar Ebola a wannan watan bayan da wata mata ta mutu ta sanadiyyar wata rashin lafiyar da ba a tantance ba amma dai tana da alamomi na cutar Ebola.

 

A ranar Larabar da ta gabata ne kasar Tanzania ta sanar da WHO  cewa ba ta da wani rahoton bullar cutar,  amma dai kasar ta yi kememe ta ki ba da sahihan bayanai dangane da koke-koken da aka ce ana samu.

 

A makon jiya ma, sakataren kula da harkokin lafiya na kasar Amurka  Alex Azar ya soki lamirin kasar Tanzania na gaza ba da bayanan da a ke bukata dangane da yiwuwar bullar cutar.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply