Abdullahi Garba jani/NIB
Gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafar ƙungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo ya ce akwai yiwuwar zuwa baɗi ya yi ritaya daga buga tamaula. Sai dai Ronaldo ya ce in don ta shi ne, yana iya kai shekaru 40-41 yana taka leda.

Cristiano Ronaldo da ya taimaka wa Real Madrid lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai Champions League sau uku a jere, ya koma Juventus ne a kakar wasan bara.

Ronaldo mai shekaru 34 ya ce yana jin dadin murza tamaula a Juventus ta kasar Italiya wadda ke riƙe da kambun gasar ƙasar watau Seria A
