Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Nijeriya na kyautata zaton fara fitar da shinkafa kasashen waje nan da...

Nijeriya na kyautata zaton fara fitar da shinkafa kasashen waje nan da badi – RIFAN

158
0

Shugaban kungiyar manoma shinkafa ta Nijeriya Aminu Goronyo ya ce su na kyautata zaton fara fitar da shinkafar Nijeriya ya zuwa kasashen waje nan da shekarar badi.

Aminu Goronyo ya fada wa Daily Trust cewa gwamnatin Buhari na samun nasara sosai wajen inganta noma, ganin yadda noma musamman na shinkafa ya ke habbaka.

Ya ce a lokacin da gwamnatin Buhari ta amshi mulki, ana noma tan daya da rabi zuwa biyu a duk kadadar noma, amma yanzu ana samun tan 5 zuwa 8.

Shugaban kungiyar ya ce kusan kaso 80 zuwa 90 na shinkafar da ake ci a Nijeriya daga 2015 zuwa yamzu, duk ana noma ta ne a cikin gida.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply