Home Sabon Labari Al Ahly ta ci kyauta a gasar zakarun duniya

Al Ahly ta ci kyauta a gasar zakarun duniya

14
0

Zakarun Nahiyar Afirka Al Ahly ta girgiza babbar kungiyar Brazil Palmeiras in da ta lashe wasan neman mataki na hudu a gasar cin kofin zakarun duniya, wanda ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida, a ranar Alhamis.

Bayan shafe minti 90 ba tare da zura kwallo a ragar ko wace kungiya ba, Al Ahly ta yi nasara a bugun finareti da aka tashi da ci 3-2.

Kungiyar ta kasar Masar, Al Ahly, ta yi rashin nasara hannun Bayern Munchi da ci 2-0 a wasan da suka buga na kusa da na karshe a ranar Litinin, yayin da Palmeiras ta yi rashin nasara hannun Tigres da ci daya mai ban haushi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply