DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 6, 2026
HomeLabaraiAlbashina N503,000 ne, na manyan sakatarorin gwamnatina kuma N900,000 - Gwamnan Delta

Albashina N503,000 ne, na manyan sakatarorin gwamnatina kuma N900,000 – Gwamnan Delta

Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana cewa albashinsa na wata-wata Naira 503,000 ne, wanda ya yi ƙasa da Naira 900,000 da manyan sakatarorin jihar ke karɓa.

Oborevwori ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da gidajen bene masu ɗakuna huɗu guda 12 da aka gina wa manyan sakatarori, tare da rabon motocin aiki guda 12 ga sabbin sakatarorin da aka naɗa a Asaba, babban birnin jihar.

Gwamnan, a wani faifan bidiyo da gidan talabijin na Arise Tv ya wallafa a YouTube, ya ce gwamnatin jihar ta ƙara wa sakatarorin albashi ne bayan sun koka cewa wasu daraktoci na karɓar kusan albashi ɗaya da nasu.

Ya ce: “Lokacin da suka ce yawancin daraktoci suna karɓar kusan irin albashin da suke karɓa, sai muka ƙara musu kuɗi. A yau, albashinku Naira 900,000 ne, nawa kuma albashin Gwamna Naira 503,000 ne.”

Ya ƙara da cewa shugaban ma’aikatan gwamnati na jihar yana karɓar Naira miliyan ɗaya a wata, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Oborevwori ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen inganta walwalar ma’aikatan gwamnati tun bayan hawanta mulki, ciki har da samar da motocin aiki ga sakatarorin dindindin.

Ya ce mutane 302 sun amfana da shirin rancen motocin ma’aikatan gwamnati, yayin da wasu 119 suka amfana da shirin rancen gidaje.

Gwamnan ya kuma ce gwamnati ta samar da kayan aikin noma ga ma’aikatan gwamnati da ke son shiga harkar noma domin samun ƙarin hanyar samun kuɗin shiga da kuma inganta samar da abinci.

Haka kuma, ya ce manyan ma’aikata 450 sun samu tallafi domin halartar wani shirin horaswa na ƙarshen mako na tsawon makonni bakwai, ta hanyar haɗin gwiwa da ‘Administrative Staff College of Nigeria’.

Oborevwori ya ce naɗin sakatarorin 12 da aka yi a watan Mayu ya tabbatar da cewa kowace ƙaramar hukuma a jihar Delta tana da wakilci a ma’aikatun gwamnati.

Ya jaddada cewa an gudanar da tsarin naɗin ne bisa cancanta, ba tare da wani mutum ya ba da shawarar sunan ɗan takara ba.

Gwamnan ya kuma ce Delta na cikin jihohin farko da suka fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ƙasa, inda jihar ta amince da biyan sabon albashin gaba ɗaya bayan tattaunawa da shugaban ma’aikatan gwamnati, kwamishinan yaɗa labarai da ƙungiyar ƙwadago ta NLC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata