Home Coronavirus Algeria za ta fara rigakafin corona a Janairun 2021

Algeria za ta fara rigakafin corona a Janairun 2021

64
0

Kasar Algeria za ta kaddamar da rigakafin cutar corona duk kuwa da cewa ba ta ware kalar rigakafin da za ta yi amfani da shi ba.

Shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter.

Tebboune dai na murmurewa daga cutar corona a kasar Jamus, an kwantar da shi tun a watan Oktoba.

Yace ya umurci Pirai Ministan kasar Abdelaziz Djerad da ya kira taron gaggawa na masana domin zabar rigakafin da kasar za ta yi amfani da shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply