BBC da sauran masu sauraro, na alhinin rasuwar tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC, Mista Barry Burgess.
Barry ya rasu a ranar Asabar din da ta wuce a gidansa da ke birnin Birmingham a Birtaniya yana da shekara 72 a duniya.
Maragayin ya rasu ne ba tare da ya yi jinya ba.
Ya soma aiki da BBC a shekarar 1974 a matsayin mai hada shiri a Sashen Hausa sannan ya bar BBC a matsayin shugaban sashen a shekarar 1999.
Bayan ya bar BBC, Barry Burgess ya koma koyar da harshen Hausa a tsangayar Nazarin Afrika da Gabashin Duniya da ke Jami’ar London.
An haifi Barry Burgess ne a ranar 8 ga watan Oktoban 1948.
