Home Labarai Ali Janga ya zama kwamishinan ‘yansandan Sokoto

Ali Janga ya zama kwamishinan ‘yansandan Sokoto

50
0

Ali Janga ya zama kwamishinan ‘yansandan jihar Sokoto, inda ya karbi aiki a hannun Ibrahim S Kaoje.

A wata takarda daga mai magana da yawun rundunar’yansandan jihar Muhammad A. Sadiq tace CP Ali Janga shi ne kwamishina na 44 a rundunar ‘yansandan jihar ta Sokoto.

Ali Janga ya rike kwamishinan ‘yansanda a jihohin Kaduna, Kogi, Bauchi, kwamishina mai kula da ‘yansandan kwantar da tarzoma (Mopol) da kuma kwamishina mai kula da ayyuka a babbar hedikwatar ‘yansanda da ke Abuja.

Sanarwar tace CP Ali Janga ya fara aikin dansanda a shekarar 1990 da matsayin dansanda mai anini (ASP) kuma ya halarci kwasa-kwasai na kwarewa kan aiki da dama.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply