Rahotanni daga Zariya, jihar Kaduna na cewa Allah ya yi wa Alhaji Bashar Aminu Iyan Zazzau rasuwa a wannan rana ta Juma’a 1/1/2021.
Dcl Hausa ta samu labarin ne daga shafin #Kasar_zazzau_a_jiya_da_yau wanda ke kawo labaran da suka shafi masarautar Zazzau da ma abubuwan da ke faruwa a lardin Zazzau da kewaye.
Marigayi Bashar Aminu, na daya daga cikin waɗanda suka nemi sarautar Zazzau bayan rasuwar Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.
