Daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce al’ummar Arewa ba su da wani dalili na kin goyon bayan shugaba Bola Tinubu a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Yari ya bayyana hakan ne a birnin Legas, lokacin da ya jagoranci wasu daga cikin mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen zuwa fadar Oba na Legas, Rilwan Akiolu, domin gudanar da ganawa a shirye-shiryen zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya ce lokaci ya yi da Arewa za ta rama irin goyon bayan da Tinubu ya bai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin da yake neman shugabancin Nijeriya da kuma lokacin da ya nemi wa’adi na biyu.
A cewar Yari, Tinubu ya yi watsi da matsin lambar da wasu ’yan jam’iyyar APC suka yi masa a shekarar 2019 na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a lokacin da Buhari ke neman sake komawa kan mulki.
Ya ce Tinubu ya yi hakan ne saboda ya yi imanin cewa lokaci ya yi da Arewa za ta samar da shugaban kasa, don haka ya tsaya a bayan Buhari har zuwa ƙarshen wa’adinsa.
Yari ya ce wannan mataki na Tinubu ya kamata ya zama dalilin da zai sa ’yan Arewa su mara masa baya a zaɓen 2027 domin ya samu damar ci gaba da mulkin ƙasar.
Ya bayyana cewa, a lokacin, Tinubu ya nuna cewa muddin Buhari ya fito domin neman kuri’ar al’umma, shi ma zai kasance tare da shi har zuwa ƙarshe.
A cewar Yari, hakan shi ne abin da Tinubu ya yi, inda ya ci gaba da nuna goyon baya ga Buhari a lokacin takararsa da kuma sake zaɓensa.
Yari, wanda ke wakiltar Zamfara ta Yamma a majalisar dattawa, ya ce irin wannan goyon baya da Tinubu ya bai wa Buhari ya samar da kyakkyawan dalilin da ya sa ’yan Arewa za su rama masa da goyon baya a 2027.
Ya ce ba wai batun tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudancin Nijeriya ne kaɗai ya kamata ya sa a goyi bayan Tinubu ba, sai dai abin da ya bayyana a matsayin ayyukan gwamnatin shugaban ƙasar da kuma ƙoƙarin magance matsalolin da ya gada daga gwamnatocin baya.
“Yau, ban ga wani uzuri da zai sa mu a Arewa mu ƙi goyon bayan Tinubu domin ya ci gaba da kyakkyawan aikin da ya fara tare da kammala wa’adinsa ba,” in ji Yari.
Sanatan ya kuma ce akwai mutane masu nagarta da mutunci a Arewa waɗanda suka yi imani da adalci da daidaito, yana mai cewa za su yi iya ƙoƙarinsu domin tabbatar da ci gaba da tafiyar Tinubu.
Yari ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu zai iya dogaro da goyon bayan wasu daga cikin ’yan Arewa wajen ganin an cimma burin sake zaɓensa a shekarar 2027.
Haka kuma, Yari ya bayyana cewa Tinubu ya aiwatar da wasu muhimman sauye-sauye da sake tsara tsarin gudanar da ƙasar tun bayan hawansa mulki.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji wani yanayi mai cike da ƙalubale daga gwamnatocin baya, amma duk da haka shugaban ya fara ɗaukar matakan da suka dace domin sake fasalin wasu ɓangarorin tattalin arziki da tsarin gudanar da ƙasa.
Ya kuma jaddada cewa goyon bayan da kwamitin yaƙin neman zaɓen ke bai wa Tinubu ba ya ta’allaka ne kawai kan tsarin rabon mulki ko kuma kasancewar lokaci ya koma Kudancin Nijeriya.
A cewarsa, abin da ya fi muhimmanci shi ne imanin da kwamitin ke da shi cewa ’yan Nijeriya na son Tinubu ya ci gaba da kasancewa a kan mulki domin ya samu damar ci gaba da manufofin da gwamnatinsa ta fara.
Ya ce wannan ne ya sa kwamitin ke ƙara faɗaɗa tuntuba da ganawa da masu ruwa da tsaki a sassan ƙasar yayin da ake tunkarar babban zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Yari ya kuma bayyana cewa manufar kwamitin ita ce ƙara wayar da kan al’umma kan manufofin gwamnatin Tinubu da kuma neman goyon bayan masu zaɓe domin tabbatar da nasarar shugaban a zaɓen mai zuwa.
