Kungiyar kwallon kafa ta Kwara United ta yi cinikin dan wasan gefen Brazil Lucas Ribeiro Alves.
Punch ta rawaito cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da lokacin da zai dawo Nijeriya domin murza leda a Kwara United.
Alves ne dan wasa na biyu da Kwara United ta saya mai kwari don tunkarar gasar firimiyar Nijeriya ta 2020/2021 bayan zuwan tsohon mai tsaron ragar Super Eagles Dele Ayenugba daga kulob din Israel Hapoel Afula.
