Home Labarai Ambaliya: Ruwa ya mamaye kauyuka 20 a Kebbi

Ambaliya: Ruwa ya mamaye kauyuka 20 a Kebbi

86
0

Wata ambaliyar ruwa da aka samu a karamar hukumar Bagudo ta jihar Kebbi ta share sama da gidaje dari biyar da kauyuka ashirin tare da mamaye gonaki.

Shugaban karamar hukumar Muhammadu Hakimi Zaga a hirar sa da DCL Hausa yace yanzu haka mutanen da suka rasa muhallansu daga sassa daban-daban ne ke fitowa inda suke samun mafaka a gine-ginen gwamnati Asibitoci, makarantu da sauran su.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Kebbi Alhaji Sani Dododo ya bayyana wa DCL Hausa cewa su na kan tattara alkaluman mutanen da iftila’in ya shafa don ba su gudunmuwa.

Mataimaki na musamman ga gwamnan Kebbi kan harkokin watsa labarai Yahaya Sarki ya ce tuni gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu ya bayar da umurnin aikewa da abinci da ruwan sha da kuma gina wuraren zagayawa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply