Home Labarai Ambaliya: Sarkin musulmi ya kai ziyarar jaje a Kebbi

Ambaliya: Sarkin musulmi ya kai ziyarar jaje a Kebbi

125
0

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya kai ziyarar jaje ga gwamnati da al’ummar jihar Kebbi, kan ibtila’in ambaliyar ruwan da aka yi baya bayan nan.

Sarkin wanda ya kai ziyarar jaje ga gwamna Atiku Bagudu a Birnin Kebbi, ranar Juma’a, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tallafawa dukkan jihohin da ambaliyar ruwan ta shafa, da ma mutanen da matsalar ta rutsa da su.

A nasa jawabin gwamna Atiku Bagudu, ya ce ba a taɓa samun ambaliyar ruwa mai munin wannan ba, wadda ta shafi sama da kadada 500,000 ta gonaki a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply