Home Labarai Ambaliya ta raba mutum 129,000 da gidajensu a bana – NEMA

Ambaliya ta raba mutum 129,000 da gidajensu a bana – NEMA

77
0

Daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) Muhammadu Muhammed ya bayyana cewa mutum 68 ne suka rasa rayukansu yayinda 129,000 kuma suka yi asara sakamakon ambaliyar ruwa a wannan shekarar.

Ya bayyana hakan a Abuja, ranar Litinin yayin ganawa kan asarar da ambaliyar ta jawo a wannan shekarar a fadin kasar.

Ya kuma shaida cewa ambaliyar ta shafi dukkan jihohin kasar har da birnin tarayya, kuma ta yi barna a kananan hukumomi 320 inda ta rusa gidaje tare da shafe gonaki wanda hakan yake kawo barazana ga wadatuwar abinci cikin kasar.

Ya kuma bayyana cewa za su aiki da sauran jami’ai da ma’aikatu domin ganin an kiyaye faruwar hakan a nan gaba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply