Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar kwara ya bayyana cewa ya mika kokensa ga gwamnatin tarayya da ta kawo dauki ga mutane dubu goma sha biyar da ambaliyar ruwa ta yi wa ta’adi a jihar.
Gwamnan ya mika bukatar hakan ne lokacin da ya ke ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.
AbdulRahman AbdulRazaq ya yi bayanin cewa ambaliyar ruwan da aka yi a jihar ta yi sanadiyar asara dukiyoyi da darajarta za ta kai kimanin Naira milyan dubu goma, inda ambaliyar ta yi sanadiyar lalata daruruwan kadada ta gonaki da ke makare da amfanin gona.
