Home Kasashen Ketare Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 12 a kasar Uganda

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 12 a kasar Uganda

266
0

Abdullahi Garba Jani

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 a yammacin kasar Uganda.

Babban jami’in kungiyar a yankin, Diana Tumuhimbise ya ce sun gano gawarwakin mutane 12 a cikin ruwa, sannan aka gano wani da dan sauransa aka garzaya da shi asibiti.

Ya ce an fara mamakon ruwan saman tun da dare har wayewar garin ranar Asabar.

Kungiyar Red Cross dai ta kaddamar da shoron ceto wadanda ibtila’in ya fada ma wa, amma dai har yanzu ba ts gano adadin yawan mutanen da abin ya shafa ba.

Jaridar Punch ta rawaito cewa har yanzu tekun da ke gabashin kasar na ci gaba da tururi ba kamar yadda aka saba ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply