Home Labarai Ambaliyar ruwa ta rusa gidaje 5,200 a Kano

Ambaliyar ruwa ta rusa gidaje 5,200 a Kano

176
0

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA) ta ce aƙalla mutane 4 sun rasa rayukansu, yayin da gidaje 5,200 suka rushe sakamakon ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomin Ɗanbatta da Rogo na jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, Sale Jili, babban sakataren Hukumar ta SEMA ya ce mutane biyu sun rasa rayukansu yayin da kuma gidaje 200 suka rushe a ƙaramar hukumar Rogo kaɗai.

Ya ƙara da cewa ambaliyar ta halaka wasu mutane biyu da kuma lalata gidaje sama da 5,000 a ƙaramar hukumar Ɗanbatta.

A cewarsa, hukumar ta bada kayayyakin tallafi na kimanin ₦3.5m ga waɗanda iftila’in ya shafa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply