Home Labarai Amfani da takardun bogi: NECO ta kori ma’aikata 19

Amfani da takardun bogi: NECO ta kori ma’aikata 19

75
0

Hukumar shirya jarabawar NECO ta kori ma’aikatan ta 19 daga aiki, bayan sun amsa laifin yin amfani da takardun bogi.

A ranar Talata ne NECO ta ce hukumar gudanarwar ta, ta amince da korar ma’aikatan biyo bayan shawarar da kwamitin tantance takardun shaidar ma’aikatan ya bada.

An dai daurawa kwamitin alhakin gayyata tare da tantace ma’aikatan da ke da alamar tambaya kan takardun su.

Rahotanni dai sun nuna cewa biyo bayan ma’aikatan 19 da aka dakatar, yawan wadanda hukumar ta dakatar ya kai 89 a cikin watanni uku, idan aka hada da wasu 70 da ta dakatar a watan Nuwambar bara kan takardun bogi.

A cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da hudda da jama’a na hukumar NECO Azeez Sani ya fitar ranar Talata, ya ce hukumar ta amince da korar ma’aikatan a taron ta na lokaci-lokaci karo na 52.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply