Home Labarai Amirka ta jinjinawa buhari kan yaƙi da cin hanci

Amirka ta jinjinawa buhari kan yaƙi da cin hanci

151
0

Gwamnatin Amirka ta sha alwashin goyawa kokarin gwamnatin Nijeriya baya kan yaki da cin hanci a dukkan matakai.

Shugaba Donald Trump da shugaba Buhari

Gwamnatin ta kuma yabawa kokarin shugaba Muhammadu Buhari na yaki da cin hancin.

Wannan ya zo a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin Amirka da jamhuriyar tsibirin Jersy da kuma Nijeriya.

Haka ma, shugaban kasar ya samu amincewar kasashen na dawo da sama da dala miliyan 308 da aka sace lokacin Abacha.

A shekarar 1990 ne aka sace dukiyar kasar karkashin gwamnatin shugaban mulkin sojan tare da ficewa da su kasashen waje, kuma yanzu za su dawo bayan shekaru sama da 20.

Gwamnatin tarayyar ta ce za ta yi amfani da kudaden wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban tattalin arziki a fadin kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply