Home Kasashen Ketare Amirka ta kama ƴan Korea ta Arewa kan zargin satar $1.3bn

Amirka ta kama ƴan Korea ta Arewa kan zargin satar $1.3bn

44
0

Hukumomi a kasar Amirka sun kama wasu ‘yan kasar Korea ta Arewa su uku bisa zargin shirya satar sama da Dala Biliyan daya da miliyan 300 daga bankuna da kuma wuraren kasuwanci a fadin duniya.

Ana kuma zarginsu da shigo da wani kasuwancin cryptocurrency mai alamun damfara.

An kuma kama wani dan asalin Canada da Amirka, bisa zargin sama da fadin kudade.

Dukkansu dai, ana zarginsu da hannu cikin wani harin intanet da aka kai kan cibiyar adana bayan harkokin lafiya ta Birtaniya a shekarar 2017.

Da yake sanar da zarge-zargen da ake yi masu, Babban lauyan tsaron kasar Amirka John Demers ya ce Korea ta Arewa ta zama wata cibiya ta kyankyashe ‘yanta’adda.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply