DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 10, 2026
HomeLabaraiAmnesty International na ci gaba da nuna bukatar hukunta Sanata Fadahunsi 

Amnesty International na ci gaba da nuna bukatar hukunta Sanata Fadahunsi 

Kungiyar Amnesty International Nigeria ta ce za ta nemi a ɗora alhakin kalaman da ake dangantawa da SanIsa ata Francis Fadahunsi, gabanin zaɓen gwamnan Jihar Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.

Babban Daraktan Amnesty International a Nigeria Isa Sanusi a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels ya ce ƙungiyar za ta yi amfani da lamarin a matsayin misali wajen nuna cewa dole ne a ɗora wa ’yan siyasa alhakin kalaman da za su iya haddasa tashin hankali yayin zaɓe.

Malam Isa Sanusi na mayar da martani ne kan wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda aka ga Sanata Fadahunsi, wanda ke wakiltar Osun ta Gabas, dan jam’iyyar APC, yana furta kalaman da Amnesty ta bayyana a matsayin masu tayar da zaune tsaye.

“Za mu yi amfani da shi a matsayin misali. Mun sha samun ’yan siyasa da dama suna furta munanan kalamai gabanin zaɓe,” in ji Isa Sanusi.

Ya ƙara da cewa wannan lamari ya sha bamban, saboda an samu wani mutum yana faɗin cewa, “a kashe su duk inda aka same su.”

Kalaman sun jawo suka sosai yayin da zaɓen ke ƙaratowa.

A ranar Talata ne Rundunar ’yan sandan Jihar Osun ta gayyaci Sanata Fadahunsi, sannan aka yi masa tambayoyi na tsawon kusan sa’o’i biyu a ranar Laraba.

Isa Sanusi ya ce Amnesty International za ta ci gaba da neman a ɗora alhakin duk wasu kalamai ko matakan da za su iya yin barazana ga zaman lafiya da damar jama’a na shiga harkokin siyasa.

Ya kuma ce ƙungiyar za ta kai batun ga hukumomin ƙasa da ƙasa.

“Za mu yi amfani da wannan mutum a matsayin misali domin nuna cewa rashin ɗaukar matakin hukunci kan ’yan siyasar Najeriya ba zai ci gaba ba, kuma ba za mu sake amince wa da hakan ba,” in ji shi.

Sanusi ya ƙara da cewa ya kamata a ɗauki fafutikar kawar da ƙiyayya da tayar da hankali da muhimmanci a ƙarƙashin dokokin Najeriya da kuma ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa.

Ya ce Amnesty za ta ci gaba da matsa wa hukumomin da abin ya shafa lamba domin su ɗauki matakin da ya dace a duk lokacin da aka samu kalaman ’yan siyasa da ake ganin za su iya ƙarfafa tashin hankali.

Ƙungiyar ta yi gargadin cewa irin waɗannan kalamai za su iya ƙara dagula yanayin siyasa gabanin zaɓen gwamnan jihar Osun.

“Dole ne a ɗora wa Sanata Fadahunsi alhakin kalamansa,” in ji Amnesty International Nigeria.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata