DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 10, 2026
HomeLabaraiAmnesty ta yi tir da tsare matasan da aka ce sun wallafa...

Amnesty ta yi tir da tsare matasan da aka ce sun wallafa kason FAAC na ƙaramar hukumarsu ta Facebook a jihar Borno

Kungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da tsare Salihu Yahaya, Haruna Mohammed da Muhammed Mallum da ’yan sanda suka yi, bisa zargin wallafa wani rubutu a Facebook kan yadda ƙaramar hukumar Shani ta karɓi kusan naira biliyan 3.11 daga aasusun rarraba kuɗaɗen tarayyar Nijeriya FAAC, tsakanin watan Janairu da Yuni na shekarar 2026.

Ko da yake daga bisani an sake su, Amnesty International mail rajin kare hakkin dan Adam ta ce tun farko kama su da tsare su da aka yi, ya saɓa ƙa’ida.

Kungiyar ta ce gwamnatin jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙaramar hukumar Shani Hassan Abdu Labaki, bai kamata ta sake yin irin wannan yunƙurin na tauye haƙƙin jama’a na neman a yi wa gwamnati bincike ba.

A cewar Amnesty International, an yi wa matasan uku tambayoyi masu tsauri da ban mamaki a lokacin da suke tsare, duk saboda sun wallafa bayanan da aka samo daga majiyoyi masu inganci game da kuɗaɗen da aka karɓa a madadin ƙaramar hukumar.

Amnesty international ta ce abin da ya faru ya nuna cewa gwamnatin jihar Borno na amfani da ’yan sanda wajen tsoratarwa da musgunawa matasan da ke neman a yi wa gwamnati hisabi.

Ta jaddada cewa neman shugaban ƙaramar hukuma ya yi bayani kan biliyoyin nairorin da aka karɓa a madadin al’umma ba laifi ba ne.

Amnesty International ta kuma ce matasan ba su aikata wani laifi ba, kuma kama su ya nuna yadda aka yi amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba.

Ta ce kowane ɗan ƙasa yana da haƙƙin karɓa da yaɗa bayanai ko kuma sukar duk wani jami’in gwamnati, ba tare da la’akari da matsayinsa ko mukaminsa ba.

Kungiyar ta kuma yi kira ga ’yan sandan Najeriya su riƙa bin ƙa’idojin doka, maimakon zama kayan aikin ’yan siyasa wajen kama da kuma tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba, ko kuma tauye haƙƙinsu na faɗin albarkacin baki da bayyana ra’ayinsu.

Kungiyar ta Amnesty ta ƙara jaddada cewa gwamnatin jihar Borno ya kamata ta riƙa kare tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam, maimakon ci gaba da kai wa matasa hari saboda amfani da haƙƙoƙinsu na asali.

A ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa na kare haƙƙin ɗan Adam, kasancewar wani rubutu a kafar sada zumunta bai yi wa shugaban ƙaramar hukuma ko wani jami’in gwamnati daɗi ba, ba dalili ba ne da zai sa ’yan sanda su tsare mutum ba bisa ƙa’ida ba inji Amnesty International.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata