DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeKetare'Amurka ta mallaki mafi yawan arzikin man fetur na Venezuela'

‘Amurka ta mallaki mafi yawan arzikin man fetur na Venezuela’

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce gwamnatinsa ta kulla wata babbar yarjejeniyar mai da Venezuela wadda ta bai wa Amurka ikon mallakar mafi yawan kaso na rijiyoyin da ke dauke da ganga biliyan 65 na man fetur da aka tabbatar da kasancewarsa.

Trump ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “yarjejeniyar mai mafi girma a tarihin duniya”, inda jami’an Amurka da Venezuela suka ce za ta jawo zuba jarin kusan dala biliyan 100 a Venezuela.

A cewar rahoton AFP, Trump ya ce yarjejeniyar za ta kara yawan arzikin man Amurka fiye da sau biyu, yayin da shugabar rikon kwarya ta Venezuela, Delcy Rodriguez, ta tabbatar da yarjejeniyar da ta kira “yarjejeniya mai tarihi”.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Rodriguez ta ce yarjejeniyar za ta taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin Venezuela, yayin da ta yi hasashen samun zuba jari sama da dala biliyan 100 da kuma sama da dala biliyan 209 na kudaden haraji ga gwamnati.

Trump ya ce yarjejeniyar ta samu ne ta hannun sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, da sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, tare da Rodriguez, ta hanyar haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu.

Sai dai har yanzu akwai tambayoyi kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar, musamman yadda za a mika ikon mallakar kadarorin man zuwa wata kasa. Masanin makamashi, Jorge Pinon, ya ce ba a fayyace ko yarjejeniyar sayar da kadarorin ce, ko kuma za a mika su ne bayan an fara hako man.

Venezuela ce ke da mafi yawan arzikin man fetur da aka tabbatar a duniya, yayin da rahotanni suka ce kasar na da ganga biliyan 300 na man fetur da aka tabbatar.

Trump ya dade yana bayyana bukatar Amurka ta kara samun damar amfani da man Venezuela. Kamfanonin Amurka kuwa suna nuna damuwa kan lalacewar ababen more rayuwa da kuma matsalolin tsaro da suka shafi zuba jari a kasar.

Kamfanin Chevron, wanda shi ne kamfanin man Amurka daya tilo da ya ci gaba da aiki a Venezuela kafin hambarar da tsohon shugaban kasar, Nicolas Maduro, ya ce a watan Yuli ya kara hakar danyen mai zuwa ganga 280,000 a rana.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata